✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai hari hedikwatar ’yan sandan Adamawa

Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari kan hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Adamawa

Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari kan hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Adamawa.

Rugugin luguden harbe-harben maharan a cikin dare ya jefa mazauna garin Jimeta da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa a jihar cikin tashin hankali.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya cewa hedikwatar rundunar ce aka kai wa hari, kuma ba a kai ga gano maharan ko manufarsu ba.

Sai dai ya bayyana cewa jami’an rundunar sun yi nasarar fatattakar maharan, bayan musayar wuta ta kusan minti 30 da misalin karfe 11 na daren Talata.

Wasu majiyoyi dai sun yi zargin maharan sojoji ne suka kai harin daukar fansa kan hedikwatar rundunar kan kisan wani hafsan soja da wani dan sanda ya yi.

Kawo yanzu dai ana bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.