Gwamnatin tarayya ta ce tuni shirye-shirye su ka yi nisa tsakaninta da shugabannin kotuna don kafa kotunan musamman don hukunta masu fyade da sauran laifukan da suka shafi cin zarafin mata a Najeriya.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami wanda ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja ya ce hakan zai taimaka wajen gaggauta yanke hukunci ga masu aikata laifin.
Ministan na jawabi ne yayin wani tattaki da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Kasa ta shirya kan matsalar fyade da sauran laifukan da su ka shafi mata.
Ya ce idan aka yi nasarar kafa kotunan, dukkan shari’u da ke gaban alkalai da ma wadanda za su zo nan gaba za a iya kammala su cikin kankanin lokaci.
Malami, wanda babban sakataren ma’aikatar kuma babban mai shigar da kara na gwamnati, Dayo Akpata ya wakilta, ya ce tuni ofishinsa ya fara nazarin dokokin da suke a kasa da suka danganci fyade, take hakkokin yara da cin zarafin mata a Najeriya.
Yayin da ma’aikatar ta ziyarci ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya jinjina wa kokarin nasu yana mai cewa gwamnatin za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin kudurin ya kai ga gaci.
Lai Mohammed ce ma’aikatarsa za ta hada gwiwa da ma’aikatar mata wajen shirya gangamin wayar da kan jama’a kan matsalar.
A Babbar Kotun Tarayya kuwa, mai shari’a John Tsoho ya ce kotun na goyon bayan kudurin dari bisa dari, kuma za ta yi aiki da su kafada-da-kafada har sai an kawo karshen matsalar baki daya.
Alamar girman matsalar a Najeriya
A wani labarin kuma, Babban Sakataren Hukumar ta Kare Hakkin Bil’adaman, Tony Ojukwu ya ce yadda mutane suka yi Allah-wadai da murya daya kan yadda matsalar fyade da cin zarafin mata da kananan yara ta yi sanadiyyar wasu daga cikinsu ya nuna girman matsalar a Najeriya.
Ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su magance duk wani nau’i na cin zarafin mata, kananan yara da masu bukata ta musamman.
Ojukwu ya kuma ja hankalin duk wadanda ke da alhakin hukunta masu laifin kamar bangaren shari’a da ‘yan sanda da su kara kokari wajen bin kadi ga wadanda su ka fuskanci matsalar.