✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da tsarin farfado da ilmi a Jihar Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya kaddamar da sabon tsarin farfado da darajar ilmi, wacce ta sukurkuce a jihar. Masu ruwa da tsaki dangane…

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya kaddamar da sabon tsarin farfado da darajar ilmi, wacce ta sukurkuce a jihar. Masu ruwa da tsaki dangane da wannan al’amari da suka hada da sarakuna da malaman makarantu da iyayen yara da makamantansu suna daga cikin mahalarta wannan taro da aka gudanar a babban zauren taro na jami’ar Ibadan (UI).

Cikin jawabinsa Gwamna Ajimobi ya ce, abun kunya ne, ganin cewa, ana samun tabarbarewar ilmi a Jihar Oyo wacce aka kafa Jami’a (Unibersity) ta farko a Najeriya.
“Wajibi ne dukkan masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen farfado da martabar ilmi a jihar. Za a iya cimma wannan nufi ne idan dukanmu muka hada hannu wajen yin watsi da matakan miyagun ayyuka na kon- konen azuzuwan makarantu da kayayyaki da zanga zangar da daliban makarantu suke yi a lokuta daban-daban,” inji shi
Gwamnan ya ce, za a bullo da tsarin kafa hukuma da za ta kunshi iyayen yara da kungiyoyin tsofaffin dalibai da shugabannin makarantu a kowace makaranta, wacce za ta rinka yin aikin tuntuba a tsakanin gwamnati da al’ummomi na kowace makarantar sakandare a jihar.
Ya ce, yin haka zai taimaka kwarai wajen cimma wannan nufi na farfado da darajar ilmi a jihar.
Da yake nuna farin cikinsa a kan yadda dukkan masu ruwa da tsaki suka amsa goron gayyatar su zuwa wajen wannan taro, Gwamnan ya ce: “Yanzu dai kowa ya fahimce mu dangane da nufinmu na lalubo hanyar daukaka darajar ilmi ne, amma ba gwanjon makarantu ba, kamar yadda wasu daga cikinku suka yi zargi a baya.”
Akwai da yawa daga cikin mahalarta taron da suka yi wa gwamna tambayoyi a kan muhimman abubuwa da suka shafi ilmi baki daya, tare da wadanda suka nuna gamsuwa da amsoshin da suka ji
daga bakin gwamnan. Kuma kowannensu ya bayar da shawarar da yake ganin za ta kai ga cimma nasara. Gwamnan ya ce za a rinka yin irin wannan taro a sauran manyan garuruwa, domin tabbatar da cewa, jama’a sun kusanci gwamnati a kan matsalolin ilmi. Haka kuma Gwamnan ya ce, daga yanzu za a fara yin jarrabawa ga malaman makarantun da suka halarci wasu kwasa-kwasai, domin tabbatar da cewa, sun cancanci koyarwa a makarantu.
Sarakunan gargajiya da suka halarci wajen taron a karkashin jagorancin Olubadan na Ibadan sun yi na’am da sabon salon farfado da darajar ilmi da gwamnatin jihar ta bullo da shi. Shugabannin makarantu da shugabannin kungiyoyin iyaye da malamai da wakilan kungiyoyin kwadago da kungiyoyin tsofaffin malamai da dalibai suna daga cikin mahalarta taron.