Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da mafarauta 1,000 da za su taimaka wajen yaki da ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar.
Da yake jawabi a kauyen Khaddamari na Karamar Hukumar Jere ta Jihar ranar Alhamis, Gwamna Zulum ya yaba wa sadaukarwar mafarautan a kokarin da ake yi na dawo da zaman lafiya a Jihar.
- Gwamnatin Kaduna ta sake maka El-Zakzaky a kotu
- ‘Akwai yiwuwar kudin kiran waya da na data ya karu a Najeriya’
Ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta samar musu da dukkan kayayyakin aikin da suke bukata da kuma kudaden alawus-alawus don gudanar da ayyukansu.
Ya ce, “Abin da muke yi a yau shine kaddamar da mafarauta 1,000 domin aikin kare manoma a Kananan Hukumomi hudu na Jihar.
“Yankunan sun hada da Maiduguri da Jere da Mafa da kuma Konduga,” inji Zulum.
Ya kuma yaba wa dan Majalisar Tarayya daga Jihar, Hon. Ahmed Satomi da takwarorinsa na Majalisar Jihar a yankunan da lamarin ya shafa saboda hado kan mafarautan da kuma sadaukarwarsu.
Tun da farko dai, dan majalisa Satomi ya ce sai da jami’an tsaro suka tantance mafarautan kafin a dauke su.
Ya ce hakan ya dace da manufar gwamnatin Borno wajen bunkasa al’amuran tsaro a Jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Gwamna Zulum ya ziyarci yankunan Mulai da Dalwa da ke wajen birnin Maiduguri inda ya gana da jami’an tsaro, a yunkurin da ake yi wajen sake bude gonakin yankin don gujewa asarar rayuka.
Zulum ya ce hakan kokari ne na bin umarnin Gwamnatin Tarayya da na sojoji wajen aiki da Jihar don ganin manoma sun koma gonakinsu. (NAN)