✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kaddamar da littafin rayuwar Aisha Buhari

An kaddamar da littafin a daidai lokacin da Shugaba Buhari yake ganin likitocinsa a Landan.

A ranar Alhamis ne aka yi taron bikin kaddamar da littafin rayuwar Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari.

Dokta Hajo Sani, babbar mai taimaka wa Shugaban Kasa ta musamman kan harkokin mata, ita ta wallafa littafin wanda aka kaddamar a wani kasaitaccen biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Sanarwar da mai taimaka wa uwargidan shugaban kasa kan yada labarai, Aliyu Abdullahi ya fitar ta ce, Dokta Hajo ta wallafa littafin ne domin girmama Hajiya Aisha Buhari.

An kaddamar da littafin mai suna, “Aisha Buhari, Being Different” ma’ana “Aisha Buhari wacce ta zama daban, a daidai lokacin da Shugaba Buhari yake ganin likitocinsa a Landan.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya wakilci Shugaba Buhari yayin bikin.

Aisha Buhari tare da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma mai dakinsa, Dolapo Osinbajo a wurin bikin
Aisha Buhari tare mai dakin Mataimakin Shugaban Kasa, Dolapo Osinbajo a wurin bikin

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da mai dakinsa, Dolapo da jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.