Shugaban Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya ja kunnen alkalai kan su kauce wa karbar na goro.
Ya kuma bukace su da su fara gudanar da zaman kotuna ta fasahar intanet domin tafiya da zamani.
Mai shari’ar ya yi gargadin ne yayin bikin rantsar da sabbin alkalai da kadi-kadi da Cibiyar Shari’a ta Kasa ta shirya ta fasahar bidiyo ranar Litinin.
Ibrahim ya ce yayin gudanar da shari’ar ta yanar gizo, dole alkalai su tabbatar suna yin adalci.
Ya ce, “A matsayinmu na alkalai da aka dorawa nauyin gudanar da sharia bisa doron doka, dole ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tunatar daku cewa duk abinda za ku yi ko dai a ciki ko a wajen kotuna dole ne ya dace da tanade-tanaden doka.
“Kazalika, dole ne ku bi tsarin doka kamar yadda kundin tsarin dokokin ma’aikata ya tanada kuma yake kunshe a sadara ta biyar ta tabbatar da nagarta a ayyukan gwamnati”, inji shi.