✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An horar da malaman firamare 3,500 na musamman a Kaduna

Kimanin malaman firamare 3,500 aka horar kan sabuwar hanyar ba da ilimi ta hanyar wake ga dalibai ’yan aji daya a fadin Jihar Kaduna. Malam…

Kimanin malaman firamare 3,500 aka horar kan sabuwar hanyar ba da ilimi ta hanyar wake ga dalibai ’yan aji daya a fadin Jihar Kaduna.

Malam Dahuru Anchau, Mataimakin Darakta mai kula da makarantu masu zaman kansu, karkashin ma’aikatar ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna,ya sanar da haka yayin da yak yine zagayen gani da ido a makarantar Malam Jalo da ke Rigachikun Jihar Kaduna, a makon da ya gabata

Ya sanar cewa, malaman su 3,500 an zakulo su ne daga makarantu daban -daban a fadin Jihar Kaduna, wanda suka samu horo kan yadda za su inganta koyar da dalibai ’yan aji daya na makarantun firamare a fadin Jihar Kaduna

Dahuru ya bayyana cewa kimanin Naira Biliyan Shida  aka ware don samar da kayan aiki da horar da malamai wanda ke karkashin wata hukuma mai suna Global Partnership For Education (GPE).

Ya kara da cewa kudin wanda aka kasafta don tafiyar da karatun cikin shekara hudu, wanda a cewarsa ana zangon shekara uku a cikin shirin.

Da take tsokaci a kan shirin, Shugabar Makarantar Malam Jalo Model, Rigachukun, Malama Asabe Danlami ta sanar da cewa kashi 70 daga cikin 100 na daliban aji daya na  firamare sun iya karatu da rubutu ta hanyar wake.

Ta kara da cewa wannan sabon  tsarin karatun ya ciyar da ilimi gaba a fadin Jihar Kaduna ta yadda dalibai ’yan aji daya kan iya hada kalmomi da karantasu ta hanyar wake da rawa.

A don haka ta yaba wa Hukumar Ilimi Karkashin  Gwamnatin Jihar Kaduna don irin namijin kokari da take yi don ciyar da ilimi gaba.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, wani dalibi dan aji daya Muhammad Abdullahi da ke Makarantar Malam Jalo Model Firamare da ke Rigachikun ya sanar da cewa ya iya hada kalmomi da karantawa ta hanyar wake.

Ya bayyana cewa wannan tsarin karatun ya ba su dama ta yadda kusan dukkan abokan karatunsa sun iya hada baki da karantawa.

Abdullahi ya jinjinawa malamansu irin jajircewa da suka yi da ba da lokacinsu wajen tabbatar da daliban sun iya hada kalmomi da karatu.

Da take nata tsokacin Hajiya Halima Jumare Babbar Darakta a Ma’aikatar Ilimi Kimiyya da Fasaha Jihar Kaduna, Hajiya Halima Jumare ta sanar cewa tsarin ya yi  tasiri matuka,  kuma ya habaka hanyar koyarwa a makarantu.

Ta kara da cewa dalibai ’yan aji daya na daukar karatu da sauri, sannan sun iya hada kalmomi da karantawa ta wannan sabon tsarin.

Halima Jumare ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin Gwamna Nasiru Ahmed El-rufai ta yadda ya ya ba ilimi muhimmanci a fadin Jihar Kaduna.