✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe Shugaban Chadi, Idriss Deby

An harbe Shugaba Deby a filin daga.

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby Itno, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Talata kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.

Rundunar ta ce ya mutu ne bayan samun raunuka a fagen daga lokacin da yake jagorantar sojin kasar wajen tunkarar ’yan tawaye da suka tayar da hargitsi a N’dajamena, babban birnin kasar.

Mai yankan kauna ta katse hanzarin Shugaba Deby ne bayan an ayyana shi a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar karo na shida a watan da muke ciki na Afrilu.

Shugaba Deby, wanda ya shafe tsawon shekaru 30 yana mulkar kasar, ya sake neman tazarce a wa’adi na shida.