✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe mutum daya a Makarantar Jangebe

Rikici ya barke a Makarantar GGJSS Jangebe a yayin da daliban da aka sako ke haduwa da iyayensu

An harbe mutum daya bayan wani rikici da ya barke a garin Jangebe inda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai mata 279 a Jihar Zamfara.

Wani mazaunin garin ya ce jami’an tsaro sun bindige wani matashi ne a lokacin da suke kokarin kwantar da tarzomar da ta tashi a makarantar a yammacin ranar Laraba.

Rikicin da ya yi sanadiyar rasa ran ya barke a Makarantar GGJSS Jangebe ne a yayin da Gwamnatin Jihar Zamfar ke mika daliban da aka sako ga iyayensu.

A ranar Laraba ne aka kai daliban harabar makarantar domin haduwa da iyayensu bayan Gwamnatin Jihar ta sa an duba lafiyarsu bayan masu garkuwa da su sun sake su ranar Talata.

Ana cikin haka ne wasu fusatattun matasa suka rika kai wa mutane farmaki a harabar makarantar.