✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe Kwamishina, an yi awon gaba da shugaban Karamar Hukuma a Kogi

Duka su biyun dai an kai musu hari ne a garin Erukutu dake kan iyakar jihar da Kwara da yammacin ranar Asabar.

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe Kwamishinan Harkokin Fansho na jihar Kogi, Mista Solomon Adebayo har lahira, yayin da Shugaban Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, Pius Kolawole ya yi batan dabo.

Duka su biyun dai an kai musu hari ne a garin Erukutu dake kan iyakar jihar da Kwara da yammacin ranar Asabar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Williams Aya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kwamishinan ya riga mu gidan gaskiya ne bayan harsashin maharn ya same shi.

To sai dai kakakin ya ce ba zai iya tabbatar da ko maharan ’yan fashi da makami ne ko masu garkuwa da mutane ko kuma ’yan bindiga ba.

Sai dai ya ce rundunar tasu ta lashi takobin ganin ta zakulo dukkan masu hannu a cikin lamarin.

ASP Williams ya ce tuni aka garzaya da gawar mamacin zuwa dakin adana gawarwaki, yayin da shi kuma kwamishinan har yanzu ake ci gaba da binciken inda ya shiga.

“Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Kogi, Mista Ede Ayuba ya umarci a aike da da dakaru domin kubutar da shugaban Karamar Hukumar daga hannun masu garkuwar da shi. Rundunarmu zata hana idanunta bacci har sai ta kubutar da shi,” injin kakakin.