An bundige jagoran wani gungun ’yan fashi tare da cafke ragowar a yayin da suke aikata fashi a yankin Ubiaja na Karamar Hukumar Esan ta kudu a Jiha Edo.
’Yan sanda da jami’an sintiri da ke kai-komi a yanki ne suka kame ragowar ’yan fashin guda uku.
Zamfara: ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Talata Mafara
Arewa ta kira taron tsaro bayan ‘katobarar gwamnati’ kan kisan Zabarmari
An bayar da belin wanda ake zargi da yin garkuwa da ’yarsa
Da sanyin safiyar Lahadi ne ’yan fashin suka far wa cibiyar lafiya ta Ogbeide da ke yankin, suka yi wa ma’aikata da majinyata fashi.
Suna tsaka da fashin ne wani daga cikin mutanen ya kira jami’an tsaron da ’yan banga da ke kula da yankin ya sanar da su halin da ake ciki.
Kafin a cafke su, ’yan fashin sun yi musayar wuta da jami’an tsaro har ta kai ga kashe jagoran gungun nasu.
Tuni aka tisa keyar ragowar ’yan fashin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Ubiaja don ci gaba da bincike, gawar mamacin kuma aka kai ta mucuwari.
An gano cewa daya daga cikin ’yan fashin da aka kama tsohon mai laifi ne da aka sako daga gidan yari bayan ya kammala zaman kaso a kwanakin baya.
Daga cikin kayan da aka samu a hannunsu akwai bindiga kirar gida da harsasai da wayoyin hannun da dai sauransu.
Majiyarmu ta ce an yi ta neman jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar, SP Chidi Nwanbuzor, ta waya amma abun ya ci tura —an kira shi amma bai amsa ba.