Hukumomin kasar Rwanda sun haramta amfani da lasifika wajen kiran Sallah a Kigali, babban birnin kasar, saboda ta rage abin da suka kira ‘hayaniya ga muhalli’.
Hukumomin sun ce kiran sallah a masallatan da lasifika ya saba dokar nan da ta hana hayaniya a cikin jama’a.
- Rikicin manoma da makiyaya ya sake yin ajalin mutum 9 a Jigawa
- Matsalar tsadar kayan abinci duk duniya ce ba iya Najeriya ba – Lai Mohammed
Gwamnatin kasar dai ta ce sai dai Musulman kasar su saka kararrawar waya idan suna son su tuna lokacin sallah.
Sai dai wasu musulmin kasar na zargin cewa an tauye musu ’yancin yin addini, la’akari da cewa ba dukkan Musulman ba ne suka mallaki wayar salula.
Manufar gwamnatin dai ita ce ta inganta birnin na Kigali din ya zama daya daga cikin manyan birane a Afirka a bangaren zuba jari da yawon bude ido nan da shekaru 22 masu zuwa.
An bullo da matakai da dama dai, amma bisa ga dukkan alamu na hana amfani da lasifikar wajen kiran Sallah ya fi tayar da kura.
Musulman birnin dai tuni suka fara bin umarnin, kodayake sun soki lamirinsa, inda suka ce kamata ya yi a ce su rage sautinsu a maimakon haka.
Sai dai matakin ba iya masallatai kawai zai shafa ba, saboda ko a watan da ya gabata sai da aka rufe coci-coci kusan 700, saboda saba wa umarnin.