✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta hawan babur a kananan hukumomi 15 a Legas

A ranar Litinin gwamnatin Legas ta fitar da sanarwar haramta hawan babur da aka fi sani da acaba ko okada da babur mai kafa uku…

A ranar Litinin gwamnatin Legas ta fitar da sanarwar haramta hawan babur da aka fi sani da acaba ko okada da babur mai kafa uku (Kake Napep) a kananan hukumomi 15 na jihar da kuma daukacin manyan hanyoyin jihar da saman gadoji.

A wani mataki da gwamnatin tace na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ne kana za a tabbatar an fara bin wannan sabuwar doka daga ranar 1 ga watan gobe.

Kwamishinan yada labarai da tsare-tsare na jihar Gbenga Omotosho, ne ya bayyana hakan a sa’ilin taronsa da manema labarai, ya ce gwamantin jihar ta kai ga daukar matakin ne bayan ta gana da masu ruwa da tsaki a fannin da majalisar jami’an tsaron jihar.

Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hadar da karamar hukumar Apapa da Apapa Iganmu LCDA sai  Lagos Mainland da Yaba LCDA da kananan hukumomin Surulere  Itire-Ikate sai Coker-Aguda LCDAs, sai Ikeja, Onigbongbo da Ojodu LCDAs; da kananan hukumomin Eti-Osa da Ikoyi-Obalende, sai Iru/Victoria Island LCDAs, da karamar hukumar Lagos Island da kuma Lagos Island East LCDA.

Yace matakin wani share fage da aka soma da kananan hukumomi 15 domin ganin an tsaftace sashin sufuri a Legas.