✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An haramta amfani da amsa kuwa da gilashin mota mai duhu a Zamfara

Rundunar ’Yan sanda reshen Jihar Zamfara ta bayar da sanarwar hana amfani da amsa kuwa ga motocin da basu samu sahalewa a hukumance ba. Kwamishinan…

Rundunar ’Yan sanda reshen Jihar Zamfara ta bayar da sanarwar hana amfani da amsa kuwa ga motocin da basu samu sahalewa a hukumance ba.

Kwamishinan ’yan sandar Jihar, Abutu Yaro wanda ya bayar da sanarwar dakatarwar a ranar Litinin ya ce za ta fara aiki ne nan take.

Sauran abubuwan da sanarwar dakatarwar ta kunsa sun hada da haramta amfani da gilashin mota mai duhu mara rajista da lambar mota ta bogi a fadin Jihar.

Kwamishinan ya ba dukkan Kwamandojin shiyoyi da Shugabannin Caji ofis na Jihar umarnin ganin sun tabbatar an kiyaye abin da sanarwar ta kunsa sau da kafa da kuma sauran dokokin da suka shafi tuki a fadin Jihar.

%d bloggers like this: