✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An haramta acaba a wasu sassan birnin Legas ‘har abada’

Gwamnan ya kuma bukaci ’yan sanda su tabbatar da bin dokar

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da haramta sana’ar acaba a Kananan Hukumomi shida na Jihar har abada.

Gwamnan ya sanar da haramcin ne bayan taron da ya yi da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar a ranar Laraba.

Babajide ya a ce haramcin ya shafi Kanana Hukumomin Ikeja da Surulere xa Eti-Osa da Lagos Mainland da Lagos Island da kuma Apapa.

Ya ce haramci ne na har abada, inda ya bukaci ’yan sanda su tabbatar ana bin umarnin yadda ya kamata.

Daukar matakin dai ba ya rasa nasaba da kisan wani matashin mawaki da ake zargin ’yan acaba sun yi inda suka kone gawarsa saboda wata takaddama kan Naira 100 a ranar Alhamis din da ta gabata.