✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana ’yan wasa ‘durkusa gwiwoyi a kasa’ kafin fara wasanni a gasar Firimiya

An hana ’yan wasan da ke bugawa wasanni a gasar Firimiya ta Ingila daga yin dabi’ar nan ta durkusar da gwiwoyinsu a kasa da suke…

An hana ’yan wasan da ke bugawa wasanni a gasar Firimiya ta Ingila daga yin dabi’ar nan ta durkusar da gwiwoyinsu a kasa da suke yi kafin a fara wasa.

Dakatarwar na kunshe a cikin a wata sanarwa da hukumar kula da gasar ta fitar a inda take cewa daga yanzu ba a kowanne wasa ne za a rika yin hakan ba.

Sanarwar wacce aka wallafa a shafin yana gizo na hukumar mai dauke da sa hannun mai horas da ’yan wasan na cewa, “Mun tsayar da shawarar zabar wasu muhimman lokuta ne na yin wannan tsuguno a kakar wannan wasannin, don nuna goyon bayanmu na kawo karshen duk wani nau’in nuna wariyar launi fata”.

’Yan wasan da ke buga kwallo a gasar Firmiya ta kasar ingila sun soma durkuso ne kafin a soma wasa a watan Yunin shekarar 2020, wata guda bayan kisan George Floyd mai alaka da wariyar launin fata a Amurka.

Tsohon dan wasan baya Colin Kaepernick ne ya soma wannan durkuso a matsayin bara’a ga kisan bakaken fata na rashin adalci a 2016.

A yanzu wannan darkuso kafin wasa ya soma daina tasiri, a cewar wasu ’yan siyasa masu sassucin ra’ayi na Ingila.