Jami’an tsaron da gwamnatin Jihar Kaduna ta jibge sun hana gungun daliban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ke zanga-zanga a yunkurinsu na zuwa Gidan Gwamnatin Jihar.
Daliban dai na zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu kan karin kudin makaranta da Gwamnatin Jihar ta yi musu.
- ‘Ba kisan gilla aka yi wa shugaban hukumar NECO ba’
- Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a bainar jama’a
Wakilin Aminiya ya ce daliban cikin fushi sun yi ta rera wakokin Allah-wadai yayin da suke kokarin danganawa zuwa gidan gwamnatin jihar, kafin daga bisani jami’an ’yan sanda suka taka musu birki.
Wakilin namu ya shaida ganin motocin jami’an tsaron cike da damara tare da ’yan bangar gwamnatin jihar na KADVIS, suna sintiri kan manyan titunan birnin domin shirin ko-ta-kwana yayin da daliban suka yi zaman-dabaro a tsakiyar titunan.
Idan za a tunawa, Gwamnatin Jihar da hukumar makarantar sun yi tsayuwar gwamin jaki ta hanyar kin soke karin kudin makarantar, duk da rokon da dalibai da ma iyayensu suka yi ta yi a jihar.
Guda cikin wakilan daliban Kwamred Ayuba Mohammed, ya ce suna kan hanyarsu ta Gidan Gwamnatin ne da zimmar mika wa Gwamna Nasir El’rufa’i takardar kokensu.
Ya ce galibin daliban marayu ne sannan iyayensu ba sa iya daukar nauyin karatunsu.
A cewarsa, “A kan hanyarmu ta zuwa gidan gwamnatin ne jami’an tsaro suka tare mu.
“Mu masu bin doka da oda ne; kawai muna son isar wa Gwamnatin Jihar sakon adawa da karin kudin makarantar.
Sai dai duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi domin jin ta bakin kakakin jami’ar, Adamu Bargo ya ci tura sakamakon ba a iya samun sa a wayar salula ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.