✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matashin da ake zargi da kwace jakar mata a kotu

Wani mutum mai shekaru 37 ya bayyana gaban kotun Majistare da ke okitipupa a Jihar Ondo, bisa tuhumarsa da laifin kwace jakar wata mata mai…

Wani mutum mai shekaru 37 ya bayyana gaban kotun Majistare da ke okitipupa a Jihar Ondo, bisa tuhumarsa da laifin kwace jakar wata mata mai dauke da wayar hannu da kudi.

Lauyan wadda ke kara ASP Zedekiah Orogbemi ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Mayu da karfe 1:30 na rana a unguwar Oke-Iloro da ke garin Okitipupa a Jihar Ondo.

Oregbemi ya ce wanda ake zargin ya fizge jakar matar da ke dauke da wayar hannu da kudi daga hanuun matar mai suna Adeola Ikuemelo, kuma take mutanen da ke kusa suka kamo shi.

Oregbemi ya ce laifin da ake zargin mutumin da shi na sata, ya sabawa sashi na 390(9) na kundin manyan laifukan shekarar 2006 na jihar Ondo.

To sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun Chif Majistare Chris Ojuola ya ba da belin wanda ake tuhumar  kan N100,000 da kuma sharadin mamallakin makamantansu zai tsaya masa.

Haka zalika kotun ta ce mai tsaya masan dole sai ya cika ka’idar kotun ta gabatar da shaidar biyan harajin Jiha na shekara biyu ga rajistaran kotun kafin ba da belin, tare da dage sauraron karar zuwa ranar shida ga watan Yuli.