An gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Shari’ar Musulunci bayan ya shafe kwana 12 a tsare, kan zargin batanci ga Manzon Allah (SAW).
Tuni Alkalin Kotun Musuluncin da ke Kofar Kudu a birin Kano, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya umarci malamin da ya shiga wurin tsayawar wanda ake kara, bayan jami’an Hukumar kula da Gidajen Yari sun kawo shi a zaman kotun na safiyar Laraba.
Gabanin Babbar Sallah ne jami’an tsaro suka cafke Abduljabbar bisa zargin sa da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) da Sahabbai da kuma yunkurin tayar da fitina.
An kama shi ne bayan Gwamnatin Jihar ta kai karar sa, bisa zarge-zargen da a kansu aka gudanar da mukabala tsakanin Abduljabbar din da wasu malaman Kano.
Bayan mukabalar, alkalinta, Farfesa Salisu Shehu ya sanar cewa Abduljabbar ya kasa amsa tambayoyin da aka yi masa kan mas’alolin da ake zargin sa a kai, sai kame-kame yake yi.
Farfesa Salisu Shehu ya kuma shawarci Gwamantin Jihar Kano da ta dauki matakin da ya dace a kan al’amarin.
Bayan nan ne Abduljabbar ya fito ya nemi afuwar al’ummar Musulmi a wani salo da ake gani a matsayin rashin laifi.
Ana cikin haka ne ’yan sanda suka gayyace shi zuwa ofishinsu, ta kuma tsare shi, Gwamnatin Jihar Kano kuma ta maka shi a gaban kuliya a ranar 16 ga watan Yuli.
Abduljabbar dai ya sha musanta zargin da ake masa na batanci ga Manzon Allah (SAW) da Sahabbai da kuma turzura jama’a.