✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An guntule kan dan kwallo a Brazil

An tsinci guntulallen kan wani tsohon dan kwallo a kasar Brazil mai suna Joao Rodrigo Silba Santos’ bayan an saka a cikin buhu sannan aka…

An tsinci guntulallen kan wani tsohon dan kwallo a kasar Brazil mai suna Joao Rodrigo Silba Santos’ bayan an saka a cikin buhu sannan aka ajiye a kofar shiga gidansa.

Matar marigayin ce ta gano haka jim kadan bayan ta koma gida a lokacin da take kokarin bude kofa.
Hada ido da ta yi da wani buhu ya ja hankalinta wajen budewa don ta ga abin da ke ciki, amma maimakon ta ga kaya ko wani abu sai ta hada ido da kan maigidanta.
Nan da nan ta rikice kuka ta kwala ihu da hakan ya janyo hankalin makwabta da na jami’an tsaro da ke yankin.
Matar ta ce bayan ta bar gida zuwa Rio de Jenairo a safiyar ranar Talatar da ta wuce, jim kadan da dawowa ne ta tsinci kan mijin nata a buhu a kusa da shiga kofar dakinta al’amarin da ya firgita ta.
Rahotannin da jami’an tsaro na ’yan sandan yankin suka bayar ya nuna bayan guntule kan tsohon dan kwallon, makisan sun yanke harshe da kuma idanunsa inda suke kyautata zaton aikin matsafa ne.
dan kimanin shekara 35, Santos ya yi ritaya daga buga kwallo ne kimanin shekaru biyu da suka wuce bayan ya yi buga kwallo a Brazil da wasu kulob a Honduras da kuma Sweden.
Bayan da ya bar kwallo ne ya tsunduma harkar sayar da kayan abinci masu gina jiki da kara kuzari.
Jami’an tsaro sun ce ana kyautata zaton ’yan ta’addan sun rutsa shi ne a kan hanyarsa ta komawa gida da daddare jim kadan bayan ya bar kasuwa.
Sai dai rahotanni sun alakanta kisan tsohon dan kwallon da masu tu’ammali da kwaya ganin cewa matar marigayin tana aiki ne a ofishin ’yan sandan da ke yankin.