✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gudanar da gasar kwallon dawaki a Minna

A ci gaba da wasan kwallon dawaki da ake yi a garin Minna da ke Jihar Neja, kungiyar Northburry da ke birnin Fatakwal ta lallasa…

A ci gaba da wasan kwallon dawaki da ake yi a garin Minna da ke Jihar Neja, kungiyar Northburry da ke birnin Fatakwal ta lallasa kungiyar Starsrace da ci 11 da uku da rabi.  Hazalika kungiyar kwallon dawaki ta Minna Auna ta lallasa Jos Cisse da ci tara da biyu da rabi. Haka kuma kungiyar Kaduna El-Amin ta yi nasara a kan Katsina Danmarna da ci takwas da shida da rabi.
An gudanar da wasannin ne a filin wasan kwallon dawaki da ke kan hanyar tsohon filin saukar jiragen sama na Minna a karshen makon da ya gabata.
 dan tsohon shugaban kasa na zamanin mulki soja, Alhaji Muhammed Ibrahim Babagida ne ya dauki nauyin shirya gasar.
Wasan wanda ya kayatar sosai ya samu halartar manyan baki da dama wadanda suka hada da Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da Kwamishinoninsa da sauran mukarraban gwamnati.
 An gudanar da wasan lami lafiya da ba tare da wata matsala ba, sannan kuma a hannu daya ’yan kallo sun bayyana farin cikinsu kan yadda wasan ya gudana ba tare da samun hadari ba.
Dukkanin ’yan wasan kwallon dawakin sun nuna bajinta inda suka rika kai hare-hare ga juna tare da cin kwallo bisa kwarewa.  Sauran wasannin da aka gudanar sun hada da Jos Malcomines da na Minna Tunga.