A kwanakin baya ne Sashen Koyar Da Harshen Hausa na Kwalejin Nazarin Shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano ta shirya taron bita na yini uku ga mawakan Hausa da ke Jihar Kano.
A jawabinsa na bude taron, shugaban sashen, Ibrahim Lawal Dakata, ya bayyana cewa sun shirya wannan bita ce domin zakulo kura-kurai da ke faruwa a harkar waka tare da neman hanyar gyara su. “Muna so ne a sami tabbatacciyar alaka tsakanin mawaka da mu manazarta, ta yadda za mu duba musu ayyukansu tare da ba su shawarwari, domin rashin kula da su shi ke jawo abubuwan da ke faruwa a harkar. Ba za ka iya kama mutum da laifi ba har sai ka kira shi ka ka yi masa gyara shi kuma bai dauka ba. Idan har aka kira su aka nuna musu cewa wakokin nan nasu masu kyau ne, ga hanyoyin da za su inganta su ta hanyar zamani da kuma gargajiya.” Inji shi.
Har ila yau, Dakata ya bayyana cewa za su ci gaba da shirya irin wadannan tarurruka ga mawakan har a kai ga cin ma buri wajen haifar da kyakkyawar alaka tsakanin mawakan da manazarta. “Za mu ci gaba da shirya irin wadanann tarurruka har ya zama mawakan sun kai ga karbar gyare-gyaren ko dai ba duka ba.”
Shi ma a bayaninsa, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya soki lamirin yin amfani da kayan kidan Turawa da mawakan Hausa a yanzu ke yin amfani da su. “Ba za ka iya jan hankalin wanda ba al’adarku daya da shi ba ta hanyar yin amfani da kayan kidansa. Idan Bahaushe zai yi amfani da
kayan kidansa irinsu kalangu da kukuma da sauransu zai fi yin tasiri a wurin Turawa a kan ya dauki yin amfani da fiyano da sauransu, wadanda asalinsu na Turawa ne.”
A takardar da ta gabatar mai taken ‘Kayan Kidan Hausawa Jiya Da Yau,’ Malama Zainab Umar Sale daga Sashen Hausa na Kwalejin, ta yi tsokaci game da yadda Bahaushe a yau ya ari kayan kidan Turawa yake amfani da su, inda ta ce hakan ya faru ne sakamakon cudanyar Bahaushen da bakin al’ummu. “Bahaushe ya ari kayan kidan da yake amfani da su a yau ne bayan da ya yi cudanya da bakin al’ummu lokaci mai tsawo. Irin wadanann kayan kidan sun sha banban da irin wadanda makadan gargajiya ke amfani da su.”
Aminiya ta tattauna da wasu mawaka wadanda aka yi abin dominsu, inda suka nuna farin cikinsu da wannan bita da aka shirya musu.
Sadik Zazzabi shi ne Shugaban kungiyar Mawaka ta Inuwar Fasaha. Ya bayyana taron a matsayin abin da zai kawo ci gaba a harkar sana’arsu ta waka. “Mu mawaka da makada mun karu da wannan bita da aka yi mana, domin taron ya kara mana kaimi wajen tunanin bijiro da wasu abubuwa sabbi; wadanda za su taimaka mana wajen dora wakokinmu a kan kyakkyawan tsari. Muna fatan kwalejoji da jami’oi wadanda ke nazarin harshen Hausa za su ci gaba da shirya irin wadannan tarurruka don ciyar da
adabi gaba. “
Game da yin amfani da kayan kidan Turawa da ake sukar mawakan suna yin amfani da shi, Sadik ya bayyana cewa ba laifi ba ne don mawakan sun yi amfani da kayan kidan Turawa. “Abin da nake so a fahimta shi ne, idan zamani ya zo dole haka mutum zai tafiyar da shi. Idan kin duba, su kansu mawakan gargajiyuar a yanzu sun ajiye kalangu da ganguna, sun koma shiga sutidiyo suna gabatar da wakokinsu.”
Shugaban ya yi kira ga mawaka gaba daya da su yi kokarin rajista da kungiyoyin mawaka, don a sami hadin kai a tsakanin mawakan yadda za a ciyar da harkar gaba. Haka kuma a cewarsa, shigar mawaki kungiya zai ba shi damar samun kariya game da hakkokinsa; a matsayinsa na mawaki, ba kamar idan ya tsaya a matsayin shi kadai ba.
Shi ma Mahmud Isma’il Nagudu ya bayyana cewa sun amfana daga wannan bita, domin a wajen taron an ilimintar da su a kan abin da ba su sani ba tare da tunatar da su a kan abin da suka sani game da waka. “An ce idan mutum yana da kyau ya kara da wanka, ko mutum ya san abu akwai bukatar a tunasar da shi. Babu shakka mun amfana daga wannan taro. Haka kuma ina tunanin za a sami dangantaka mai kyau tsakanin mu mawaka da su manazarta, da ayyukanmu ne suke gudanar da nasu aikin wajen gina adabi. Na tabbatar wasu abubuwan da muke yi akwai kura-kurai a ciki, yayin da wasu abubuwan ba kura-kurai ba ne; rashin fahimtar juna ne. Amma ta hanyar irin wannan tattaunawa ce za mu fahimci junanmu.”
Dangane da amfani da kayan kidan Turawa da mawakan ke yi kuwa, Mahmud Nagudu ya danganta hakan da lalura, idan aka yi la’akari da rashin isassun kudi a harkar waka.
Su ma sha’irai wato masu yabon Annabi cikin harshen Hausa ba a bar su a baya ba wajen halartar wannan taro, inda mafi yawansu suka nuna jin dadi game da wannan taron bita da aka shirya musu.
An gudanar da bita ga mawakan Hausa
A kwanakin baya ne Sashen Koyar Da Harshen Hausa na Kwalejin Nazarin Shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano ta shirya taron bita na yini uku…