Masarautar Ham da aka fi sani da masarautar Jaba da ke garin kwoi a karamar Hukumar Jaba na daga cikin fitattun masarautu a Kudancin Jihar Kaduna.
Kamar sauran kabilun da ke yankin, suna gudanar da bukukuwan al’adunsu a kowace shekara ta hanyar kade-kade da raye-rayen gargajiya tare da sauraron jawabai daga shugabanni.
Bukin na bana, wanda aka gudanar da shi a makon jiya, bai bambamta da sauran na baya ba.
A lokacin da yake jawabi, Mai martaba Sarkin kwoi, (Kpok Ham) Mista danladi Gyet Maude, ya ce masarautarsa tana da da abubuwan tarihin da suke alfahari da su da suke cike a gidajen tarihi na kasashen duniya da suka hada da shahararren gunkin nan na Nok da sauransu.
Da ya waiwayo kan batun siyasa, Sarkin ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da zabubbukan fitar da ’yan takarar shugabannin kananan hukumomin Jihar Kaduna tare da kansilolinsu ba tare da samun wata hayaniya ba, inda ya bayyana hakan da gagarumin ci gaba da kuma wayewa a kan dimokuradiyya da jama’a suka samu. “Wannan ci gaba ne a dimokuradiyyarmu, don haka nake kira ga shugabanninmu na siyasa su guji yin amfani da kalmomi na ingiza mutane zuwa ga tashin hankali,” inji shi.
Sarkin, ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda bai yi kasa a gwiwa ba wajen shawo kan zaizayar kasa da kuma motsin kasar da ta auku a garin kwoi a bara.
Da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya taron na ‘Ranar Ham’, Ambasada Bulus Lolo ya ce maimakon ware rana guda don yin raye-raye da kade-kade da sunan ranar Ham da aka fi saninsu da shi, a bana sun mayar da bikin ‘Makon Ham’ inda suka shafe tsawon mako guda suna gudanar da abubuwan da suka jibinci wannan biki da suka hada da gudanar da ayyukan kiwon lafiya kyauta da likitoci da sauran kwararrun jami’an kiwon lafiya suka gudanar ciki har da aikin ido da gudanar da addu’o’i a masallatai da coci-coci da shirya gasar kwallon kafa har zuwa ranar da suka kare da wasannin gargajiya.
Shi kuwa a nasa jawabin, Dokta Phillip Hayab, kira ya yi ga gwamnatin canji da ta canja musu sunan masarautarsu da na karamar hukumarsu daga Masarautar Jaba zuwa Masarautar Ham da kuma karamar Hukumar Ham maimakon ta Jaba da aka fi saninsu da shi domin a cewarsa, bincikensa ya nuna masa cewa Jaba kalma ce ta kaskanci da ta samo asali daga harshen Hausa da ke nufin Jaba.
Bayan dogon jawabin da ya gabatar na tarihin kabilar ta Ham (Jaba), Dokta Hayab ya yi kira ga gwamnati ta samar musu da wani kamfanin sarrafa citta da ake fitar da ita a kananan hukumomin Jama’a da Jaba da Kachiya da Kagarko da ke wanda a cewarsa, hakan zai taimaka wajen rage asarar da manoma kan yi yayin faduwar farashin citta a kasuwannin duniya.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin na bana akwai sarakunan gargajiya da ’yan siyasa.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, wanda Kwamishinan Kudi, Suleiman Abdu Kwari ya wakilta, ya yi kira ga jama’ar jihar su rungumi zaman lafiya tare da mara wa kyawawan manufofin gwamnatin jihar baya don samun ci gaban jihar.