✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An girke jami’an tsaro Sakatariyar APC a Abuja

Akalla motocin sintiri ‘yan sanda 20 ne aka ajiye a kofar shiga babbar Sakatariyar jam’iyyar APC da ke unguwar Wuse 2 a babban birnin tarayya…

Akalla motocin sintiri ‘yan sanda 20 ne aka ajiye a kofar shiga babbar Sakatariyar jam’iyyar APC da ke unguwar Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, girke jami’an tsaron a Sakatariyar nada nasaba da umarnin kotu kan dawowar Shugaban jam’iyyar APC na kasa Comrade Adams Oshiomohle, zuwa ofishinsa.

Jami’an tsaron sun dakatar da ma’aikatan sakatariyar da ‘yan jarida shiga cikin babbar sakatariyar jam’iyyar.