✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kar Ku Rika Biyan Kudin Gyaran Transfoma —Kamfanin JED

Laifi ne a nemi al’umma su ba da gudummawar kudi don gyara ko canza taransfomarsu da ta lalace

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ya shawarci abokan huldarsa a Jihar Gombe da kada su biya kowa kudin gyara na’urar taransfoma a yankunansu.

Babban jami’in tsaro na JED, Musa Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin cewa, ba hakkin kwastomomi ba ne su gyara taransfoma idan ta lalace.

Abdullahi ya ce ana sa ran jama’a su kai rahoto ofishin JED mafi kusa a duk lokacin da na’urar taransifoma ta samu matsala, kuma kada su biya wani jami’inta kudin gyara.

Ya ce ba daidai ba ne a nemi al’umma su ba da gudummawar kudi don gyara ko canza taransfomarsu da ta lalace, hasali ma yaudara ce da kamfanin ba zai lamunta ba.

Jami’in ya shawarci al’ummar jiha da su kai rahoton duk wani ma’aikacinsu da ya nuna irin wannan bukata domin daukar matakin da ya dace.

Ya ce “Ba ma karbar kudi daga hannun al’umma don gyara tiransifoma don haka babu wanda ake tsammanin zai biya.

“Duk ma’aikacin da ya je wurin al’umma karbar kudi a gida-gida ko a kan titi, yaudara ce kuma mun haramta hakan.

“Idan kuna ganin ba za ku iya jira a gyara taransfoma ba, sai ku rubuta wa Manajan Darakta ta hannun Manajan Yankinku cewa kuna son tallafa wa kamfanin don radin kanku ba tilasta muku aka yi ba.

Abdullahi ya kuma yi kira ga al’ummar Gombe da su mara wa kokarin kamfanin na kare wutar lantarki a jihar.

Sannan ya yi kira da kada a rika cin zarafin jami’an JED da ke bakin aiki, yin hakan laifi ne.