Kimanin wata 11 bayan ya yi batan-dabo, daga karshe dai an gano wani sashe na wani jirgin yaki mallakin Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya da ya bace, a Dajin Sambisa.
Rundunar Sojojin Kasa ta Najeriya wace ta tabbatar da labarin cikin wata sanarwar ranar Asabar ta ce dakarunta da ke rundunar tsaro ta Operation Desert Sanity ce ta gano sassan jirgin a dajin da ke Jihar Borno.
- ’Yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutum 11 a kauyukan Kaduna
- Kai-Tsaye: Babban Taron Jam’iyyar APC na Kasa
Jirgin, mai lamba NAF 475 dai, wanda ya bace dauke da matukansa a ciki, an ba da rahoton bacewarsa ne ranar 31 ga watan Maris, 2021.
Sanarwar ta ce, “Dakarun rundunar tsaro ta Operation Desert Sanity da ke kan sintiri a Dajin Sambisa a Jihar Borno, sun gani wasu sassa na jirgin yakin sojin saman Nigeriya (NAF475) da ya bace da matukansa ranar 31 ga watan Maris, 2021.
“Muna ci gaba da fadada bincike a kai,” inji sanarwar.