Shugaban Cibiyar Binciken Likitoci ta Najeriya, Farfesa Babatunde Salako, ya ce sun gano wata kwayar cutar zazzabin cizon sauro da ake kira ‘Anopheles Stephensi’ da ke rayuwa a Arewacin Najeriya kadai.
Salako ya bayyana cewa sabon nau’in cutar na da wahalar magancewa kuma babu inda aka taba ganin bullarsa a kusa da Yammacin Afirka ma baki daya, sai a yaznu da aka tsince ta a yankin na Arewacin Najeriya.
- ’Yan ta’adda sun kashe sojojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa a Abuja
- Matar aure ta kashe mijinta kan karin aure
Ya kuma ce, “Mun fara nazari da kungiyoyi biyar domin samar da rigakafin cutar na cikin gida, kuma burinmu shi ne ya zamanto masu binciken Najeriya ne suka gudanar da shi tun daga farko ha karshe,” in ji shi.
Ya bayyana wa manema labarai hakan ne a Legas a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa da ma’aikatan cibiyar suka shirya, in da ya ce binciken zai yi tasiri matuka wajen magance zazzabin cizon sauro a Najeriya.
Ya ce, “Muna sa rai daga yanzu ’yan Najeriya ne za su dinga samar da rigakafin duk wata annoba da ta auku a kasar, da wacce aka sani da sabuwa, domin tuni mun samar da na cutar COVID-19, kuma za mu gwada a kan mutane 2,000″.