✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano nau’in sauron da ba ya jin maganin Maleriya a Jigawa

Binciken masana daga Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa, ya gano wani nau’in sauron da ba ya jin maganin zazzabin maleriya a…

Binciken masana daga Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa, ya gano wani nau’in sauron da ba ya jin maganin zazzabin maleriya a Jihar.

Sakamakon binciken nasu ya nuna maganin zazzabin cizon sauron da aka sarrafa a jikin gidan sauron da aka raba wa jama’a ba ya yin wani tasiri a kan nau’in sauron.

Shugaban yada labarai na jami’ar, Abdullahi Yahaya-Bello, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a Dutse, babban birnin Jihar.

Sanarwar ta ce an gano hakan ne sakamakon binciken da tawagar masanan suka gudanar a tsakanin Jihohi 36 na kasar nan har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Yahaya-Bello ya ce, “A matsayin wani bangare na kokarin yaki da zazzabin Maleriya, tawagar masana daga FUD karkashin jagorancin Farfesa Mustafa Dogara, ta gano wani nau’in sauro a Jigawa wanda ba ya jin maganin kashe kwari da aka sarrafa a jikin gidan sauron da aka raba wa jama’a a Jihar.

“Sai dai da alama maganin kashe kwari na ‘Primiphosmenthyl’ da aka sarrafa a jikin wasu gidajen sauron, ya yi tasiri,” inji jami’in.

Daga nan, Yahaya-Bello ya ce masanan sun ba da shawarar cewa daga yanzu a koma amfani da gidan sauro wanda aka sarrafa da ‘Primiphosmenthyl’ a Jihar.