Kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwe Ene Okon ya ce, an gano motoci biyar da aka sace.
Okon ya ce, kusan wata daya kenan da sace motocin, ‘yan sandan dai sun yi amfani da hikima wajen bankado wadanda ake zargin cewa sun shahara wajen sace motocin jama’a daga wajen da suke ajiye wa, musamman a Makurdi babban birnin jihar da kewayen jihar.
A cikin makonni biyu kadai an gano motoci biyar da aka sace, daya daga cikin motar ta tsohon Kwamishinan ‘yan sanda ce.