✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawarwakin maza biyu a Makurdi

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta gano wasu gawarwakin maza biyu a kusa da titin jirgin kasa da ke gabar kogin Benuwe a cikin birnin…

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta gano wasu gawarwakin maza biyu a kusa da titin jirgin kasa da ke gabar kogin Benuwe a cikin birnin Makurdi a yau Laraba.

Wakilinmu ya bayyana cewa, gawarwakin da ba a iya tantance su an kashe mutanen ne ta hanyar amfani da wuka sannan aka ajiye su a gefan kogin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ya tabbatar da gano gawarwakin sannan an kai su dakin aje gawarwakin da ke babban asibitin jihar, sannan za a ci gaba da binciken gawarwakin da dalilin kisan da aikata.