✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano gawar mutum 15 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Legas

Har yanzu ana laluben gawar daya mutumin

Wani jirgin ruwa mai dauke a mutum 16 da ya kife a tekun Legas ya yi sandiyar rasuwar fasinjoji 15 daga ciki.

Babban Manajan Hukumar Kula da hanyoyin ruwa na jihar Mista Oluwadamilola Emmanuel ne ya tabbatar da hakan, in da ya ce an gano gawarwaki 14 a ranar Asabar, yayin da washe gari kuma aka gano sauran  11.

Emmanuel ya ce tawagar ceto ta musamman ce ta Hukumar, hadin guiwa da ta sojojin ruwa, hadi da ta ba da agajin gaggawa na can suna kokarin gano mutum guda da har yanzu ba a ga gawar tashi ba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa jirgin ruwan ya tashi ne da misalin karfe 7:45 na yammacin ranar Juma’a makare da fasinjoji 16, inda direban ya karya dokar hana tuka jirgi a ruwa da yamma ba tare da raba wa fasinjoji rigunan taimakon ninkaya ba.