Wani jirgin ruwa mai dauke a mutum 16 da ya kife a tekun Legas ya yi sandiyar rasuwar fasinjoji 15 daga ciki.
Babban Manajan Hukumar Kula da hanyoyin ruwa na jihar Mista Oluwadamilola Emmanuel ne ya tabbatar da hakan, in da ya ce an gano gawarwaki 14 a ranar Asabar, yayin da washe gari kuma aka gano sauran 11.
- LABARAN AMINIYA: Zabar Sanata Kashim Shettima Abokin Takaran Tinubu Ya Dace – Zulum
- Yawan mutanen duniya zai kai biliyan 8 kafin karshen 2022 – MDD
Emmanuel ya ce tawagar ceto ta musamman ce ta Hukumar, hadin guiwa da ta sojojin ruwa, hadi da ta ba da agajin gaggawa na can suna kokarin gano mutum guda da har yanzu ba a ga gawar tashi ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa jirgin ruwan ya tashi ne da misalin karfe 7:45 na yammacin ranar Juma’a makare da fasinjoji 16, inda direban ya karya dokar hana tuka jirgi a ruwa da yamma ba tare da raba wa fasinjoji rigunan taimakon ninkaya ba.