✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar ma’auratan da suka vace bayan shekara 75

Daskararrun gawar wasu ma’aurata ’yan qasar Switzertaland ya bayyana a tsauniun qanqara da ke kan tsaunukan Alps bayan vacewarsu da shekara 75, kamar yadda kafar…

Daskararrun gawar wasu ma’aurata ’yan qasar Switzertaland ya bayyana a tsauniun qanqara da ke kan tsaunukan Alps bayan vacewarsu da shekara 75, kamar yadda kafar yaxa labaran qasar suka bayyana a Talatar makon da ya gabata.

Marcelin da Francine Dumoulin, mahaifan ’ya’ya bakwai ne da suka tafi tatsar madarar shanunsu a makiyayyar da ke saman Shandolin a gundumar Valais a ranar 15 ga Agustan 1942.

Mun shafe xaukacin rayuwarmu muna nemansu ba tare da qaqqautawa ba. Mun xauka cewa za mu samu damar yi musu jana’izar da ta dace da su wata rana, “qaramar ’yarsu Marceline Udry Durmoilin ta bayyana wa Lausanne jaridar kullum ta Le Matin.

“Zan iya cewa bayan shekara 75 muna jira waxannan labarai sun sa mini natsuwa,” a cewar matar mai shekara 79.

Kwatsam wata rana jami’an ’yan sandan yankin Valais sun gano gawarwakin mutum biyu, waxanda aka gano a makon jiya yayin da wani ma’aikaci ke sululu a kan qanqara a saman  wajen shaqatawa na Les Diablerets kan tudu mai tsawon mita dubu biyu da 615.

Za a gudanar da gwajin qwayoyin halitta don tabbatar da sahihancin ma’auratan ko su wane ne.

“Gawarwakin suna kwance kusa da juna. Namiji ne da mace sanye da tufafin da ake ado da su zamanin yaqin duniya na biyu,” Berhard Tschannen, Daraktan tudun qanqara na “Glacier 3000,” ya  sanar da jarida.

“An alkinta jikinsu da kayansu tsaf,” inji shi.

“Muna tunanin sun faxa rami ne bayan da qanqara ta tsotse ta zaftare tsawon shekaru. Da qanqarar ta riqa raguwa sai ta sako jikiunsu,” kamar yadda ya bayyana a jaridar Tribune de Geneve.

Mamamatan, Marcelin Dumoulin mai shekara 40, mai sanar’ar aikin takalmi ne, ita kuwa uwargida Francine mai shekara 37 malamar makaranta ce. Sun bar ’ya’ya maza biyar da mata biyu.

“wannan ne karon farko da mahaifiyata ta tafi yawon shaqatawa tare da shi. Domin kusan kodayaushe tana xauke da juna biyu, don haka take fama da wahalar hawa tsaunin qanqara,” inji Udry-Dumoulin.

“bayan wani tsawon lokaci sai aka raba mu a tsakanin wasu iyalai. Na yi sa’ar zama tare da gwaggona,” inji ta. “Muna zaune a wannan yankin, amma mun zama baqi.”

“Dangane da jana’iza kuwa ba zan sanya baqin tufafi ba. Ina ganin fari ya fi dacewa. Domin yana nuni da fata nagari, abin da ban tava rasawa ba.”