✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano fiye da yara 50 da aka sace a wani coci a Ondo

’Yan sanda sun ce har yanzu babu wasu cikakkun bayanai game da lamarin.

’Yan sanda sun ceto fiye da yara 50 da aka sace a wani ginin coci na karkashin kasa da ke Unguwar Vanlentino a kwaryar birnin Jihar Ondo.

A wani hoton bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ji wata murya daga cikin yaran da aka sace tana cewa: “An gano yaran da aka sace a wani daki na ginin karkashin kasa na wani coci a Unguwar Valentino a Ondo.

“An kama Faston da sauran mambobin cocin kuma suna cikin motar ’yan sanda.”

Da take zantawa da manema labarai, mai magana da yawun rundunar ’yan sanda, Funmilayo Odunlami, ta ce an kai wadanda lamarin ya rutsa da su hedikwatar rundunar da ke Akure.

Sai dai ta ce har yanzu babu wasu cikakkun bayanai game da lamarin a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

“Bani da cikakken bayani tukuna, amma an kawo wadanda abin ya shafa hedikwatar,” in ji ta.