’Yan sanda sun gano tare da kwance wani sabon bom da aka dasa a wani otal da ke Unguwar Romi a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
An gano bom din ne bayan wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Lahadi tana gargadin ’yan jihar game da shirin ’yan ta’adda na dasa bama-bamai a makarantu da asibitoci da wuraren ibada da sauran wuraren taruwan jama’a.
- ’Yan ta’adda sun dasa bom a makarantu da asibitocin Kaduna
- DAGA LARABA: Yadda ’Yan Siyasa Ke Yada Labaran Karya Don Su Ci Zabe
Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta yi gargadin ne bayan fashewar wani bom a kangon wani tsohon otal da ke unguwar Kabala a garin Kaduna.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta samu rahoton wani abun fashewa ne a ranar Talata, a gidan kallon kwallon kafa da ke otal din Larry Breeze Bar, inda mutane suke taaka da kallo.
“Bisa bayanan da muka samu ne muka tura jami’an Sashen Kwararu kan Ababen Fashewa nan take, suka je suka kwance bom din cikin nasara,” inji kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige.
Ya shawarci al’ummar jihar da su ci gaba da lura da abubuwa da ke faruwa a zagayensu tare da kai rahoton duk abun da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro a kan lokaci.
Jalige ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata damuwa ba.
A cewarsa, “Tuni aka fara bincike game da bama-baman biyu domin cafko wadanda suka dasa su da nufin jefa al’umma cikin zullumi.”