✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano ɗan Boko Haram da ke ɓoye a coci

A ƙarshen makon jiya ne rundunar tsaro ta sa kai (Cibilian JTF) ta yi nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram a harabar wani coci…

A ƙarshen makon jiya ne rundunar tsaro ta sa kai (Cibilian JTF) ta yi nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram a harabar wani coci a Legas.
A cewar Mai Kanurin Jihar Legas, Alhaji Mustafa Muhammad, wanda ake zargin mai suna Adam, yana ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar Boko Haram su 100 da ake nema ruwa a jallo da rundunar sojin Najeriya ta fitar da sunayensu tare da hotunansu a watannin baya.
Ya ce an gano Adamu ne a maɓoyarsa a cikin kwantena mai tsawon ƙafa 40, wacce ke harabar wani coci da ke Unguwar Festak, Legas.
An kuma kame ƙarin wasu ’yan ƙungiyar su biyar a sassa daban-daban na Legas, waɗanda suka haɗa da Ibrahim Ali da Abubakar Ahmed da Goigoi Kamsalem. Sai kuma Ibrahim Muhammad da Babagana Bilam Ali, waɗanda aka garzaya da su Jihar Borno don ci gaba da bincike.
Mai Kanurin na Jihar Legas ya shaida cewa suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa da rundunar tsaro, kana yana da hakimai a sassan Jihar Legas, waɗanɗa duk mutumin da ya zo daga yankin Barno zai je wajansu su tantance shi kuma duk wanda ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar za a miƙa shi gare shi, a kai su ga jami’an tsaro.