Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a ranar Laraba ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a na shekarar 1444/2023.
Hakan dai na nufin za a fara azumin watan Ramadan ranar Alhamis a Najeriya.
Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce, “Yau Laraba, 29 ga watan Sha’aban, Hijira 1444, daidai da 22 ga watan Maris, 2023, an kawo karshen watan Sha’aban.
“Mun samu labarin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci a wurare da yawa a kasar nan, kuma kwamitocin ganin wata sun tantance sahihancin bayanan.
“Bisa ga haka, gobe Alhamis, 23 ga watan Maris ta zama daya ga watan Ramadan,” a cewar Sarkin Musulmi.
Ya yi kira ga al’ummar musulmi bayan kammala zaben 2023 da su dage da addu’a domin samun ci gaban kasa da Jihohi.
Ya kuma nemi masu kudi a cikin al’umma da su taimaki talakawa da gajiyayyu a lokacin ibadar azumin, musamman da abinci da sauran abubuwan bukata.