Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya ta fito da sabon tsarin rijistar littattafai ta intanet.
Sabon tsarin ya kunshi rijistar wakoki da kuma fina-finai.
Hukumar ta kaddamar da bikin bude sabon tsarin ne a Otel din Sheraton Hotel & Towers da ke Legas a ranar Juma’a 25 ga Yuli, 2014.
A wata sanarwar da Darakta-Janar din hukumar Mista Afam Ezekude ya sanya a shafin intanet din hukumar ya ce, an kawo wannan sabon tsarin ne don saukaka wa marubuta da mawaka da ’yan fim hanyar yin rijista da hukumarsu.
Sanarwar ta ce: “Sauran alfanun wannan sabon tsarin sun hada: Kowane marubuci dan Najeriya da ke zaune a ko’ina a duniya zai iya rajistar wakarsa ko littafinsa ko fim dinsa cikin sauki. Za a kare wa kowane marubuci da mawaki da mai fim kayansa, kasancewar za a mika bayanin kayayyakinsa ga Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Duniya. Za a iya samun bayanin marubuci cikin sauki daga ko’ina a duniya.”
An fara wannan rijista ne a 1 ga Agusta, 2014 inda marubuta za su cika fom bayan sun shiga shafin intanet din hukumar.
An fito da sabon tsarin rijistar littattafai ta Intanet
Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya ta fito da sabon tsarin rijistar littattafai ta intanet.Sabon tsarin ya kunshi rijistar wakoki da kuma fina-finai.Hukumar ta kaddamar…