Wasu matasa sun fille kan wani malamin tarihi da ya nuna zanen batanci ga Annabi (SAW) a lokacin da yake bayar da darasi a aji.
Rundunar ‘Yan Sandan Yaki da Manyan Laifuka ta Faransa ta tabbatar da hakan a ranar Juma’a da misalin karfe 5 na yamma.
Cin zarafin Annabi: Malaman Musulunci sun la’anci mujallar Charlie Hebdo
Sultan ya roki limaman Juma’a su yi hudubar zaman lafiya
Ta ce abin ya faru ne a wata makaranta mai suna Conflans Saint-Honorine da ke Arewacin Paris, babban birnin kasar.
Rundunar ta ce abin ya samo asali ne bayan malamin da aka fille wa kai ya nuna zanen batancin a cikin aji yayin da yake bayar da darasin tarihi.
Ta ce bayan kashe malamin ne jami’an tsaro suka yi kokarin kama matasan a hukunta su amma abun ya gagara har ta kai ga an bindige su.
Jami’an rundunar sun yi zargin “kisan na da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda da kungiyon masu aikata muggan laifuka”.
Ta kamanta lamarin da abun da ya faru a kasar a watan jiya, inda ake zargin wani mutumin Pakistan mai shekara 25 da raunata wasu mutum biyu da suka wallafa hotunan batanci ga ma’aiki (S.A.W.) a mujallar Charlie Hebdo.
Idan ba a manta ba Charlie Hebdo ta yi kaurin suna wurin wallafa hotunan batanci ga ma’aiki, lamarin da ya sa aka sha kai mata hari.
A shekarun baya, hoton batancin da ta wallafa ya sa ‘yan bindiga kai wa ofishinta hari tare da hallaka wasu daga cikin manyan masu zanenta.
Sai dai gwamnatin Faransa da masu fafutika na kare alkaba’in da mujallar ke yi da sunan ‘yan bayyana ra’ayi.
Hotunan batancin da mujallar ta wallafa sun sha ja mata la’anta daga al’ummar Musulmi tare da zanga-zanga a sassan duniya.