✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara shirin yi wa ’yan kwallon Enugu Rangers goma ta arziki

Gwamnatin Jihar Enugu ta ce shirye-shirye sun yi nisa a kokarin karrama ’yan kwallon kungiyar Enugu Rangers bayan da suka samu nasarar lashe gasar Firimiya…

Gwamnatin Jihar Enugu ta ce shirye-shirye sun yi nisa a kokarin karrama ’yan kwallon kungiyar Enugu Rangers bayan da suka samu nasarar lashe gasar Firimiya ta bana a Najeriya.
Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinan Wasanni na Jihar, Charles Ndukwe ya sanar inda ya ce Gwamnan Jihar Ifeanyi Ogwuanyi ya shirya tsaf don yi wa daukacin ’yan wasan da jami’ansu goma ta arziki a kan namijin kokarin da suka yi na lashe gasar Firimiya ta bana a karo na farko bayan shekara 32.
Sai dai Kwamishinan ya nuna da wuya gwamnatin jihar ta saka musu da kudi ko motoci sai dai a raba musu gidaje ko filaye.
Ya ce sun lura ba ’yan kwallon fili ko gida zai fi tasiri fiye da raba musu kudi ko motoci don nan gaba ko filin suka tashi sayarwa zai fi daraja fiye da motoci.  Haka kuma idan aka ba su tsabar kudi da wuya wadansu daga cikinsu su tsinana abin-a-zo-a-gani  musamman a wannan lokaci na tabarbarewar tattalin arziki.
Gwamnatin ta jinjina wa ’yan kwallon a kan daukaka martabar jihar a idon duniya ba a Najeriya kadai ba bayan sun lashe wannan kofi bayan shekara 32.
Kwamishinan ya ce tuni suka tura bukatar karrama ’yan kwallon ga ofishin Gwamnan, kuma da zarar ya amince za su sanar da duniya takamaiman ranar da za a karrama ’yan kwallon.
Enugu Rangers dai ta samu tsabar kudi Naira miliyan 40 ne daga Kamfanin da ke kula da yadda gasar Firimiya ta Najeriya ke gudana (LMC) inda tuni ya mika cekin kudin ga kulob din a ranar Lahadin da ta wuce jim kadan bayan Enugu Rangers ta lallasa El-Kanemi Warrior a wasan karshe da ci 4-0.