Wani kamfanin kere-kere a kasar Japan ya fara sayar da babur mai tashi sama da ya kirkira a kan kimanin Dala 700,000, kimanin Naira miliyan 287.
Kamfanin A.L.I Technologies ya fara kera babur din da aka sa wa suna XTurismo Limited Edition ne tun a shekarar 2017, wanda a yanzu haka aka kammala har an fara sayarwa a kasar Japan.
- Majalisa ta yi watsi da bukatar karbo bashin $200m don sayen gidajen sauro
- Yadda auren ‘talaka’ ya nesanta ’yar sarki da sarautar Japan
Shugaban kamfanin, Daisuke Katano, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za a iya keta hazo da babur din na kimanin minti 40, yana gudun kilomita 100 a cikin minti 40.
“Mun yi tunanin kera mashin din ne saboda biyan bukatar mutane masu son tuki a sama da kuma da saukaka zirga-zirga yayin kai agaji a lokacin da bukatar hakan ta taso a wuraren da motoci za su yi wahalar shiga,” a cewar shugaban kamfanin.
Ya kara da cewa suna so zuwa nan gaba masu amfani da motocin kece raini na zamani su koma amfani da mashin din.
Duk da cewa a yanzu an fara sayar da mashin din a kasar Japan an takaita zirga-zirga da shi zuwa wuraren tsere da kuma wuraren gwaji kafin daga baya gwamnati ta bayar da izinin amfani da shi a kan tituna.
A yanzu haka kofa a bude take ga duk mai bukatar sayen babur din daga ko’ina a duniya.