Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara mayar da ’yan gudun hijira zuwa garuruwansu bayan al’amuran tsaro sun fara inganta a Jihar.
Kwamishiniyar Agaji da Jin-kai ta Jihar, Hajiya Faika Ahmed ce ta sanar da hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a Gusau ranar Juma’a.
Ta ce gwamnatin Jihar ta samar da kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum ga ’yan gudun hijirar sama da 400 domin su samu su koma garuruwan nasu.
Hajiya Faika ta kuma ce ana damka mutanen ne a hannun Hakiman yankunansu.
Kwamishiniyar ta kuma kara da cewa mutanen, wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara na samun rakiyar jami’an tsaro don tabbatar da sun koma lafiya.
Ta ce rahotannin da suke samu daga jami’an tsaro na tabbatar da cewa zaman lafiya ya fara samuwa a yawancin yankunan da ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa ya daidaita.
Ta kuma ce akalla iyalai 184,000 ne matsalar tsaron ta shafa a Jihar, inda daga ciki ta ce akwai ’yan gudun hijira 600,000 a fadin Jihar. (NAN)