’Yan sanda sun fara kamen masu aron hannu idan suna tuki a duk fadin Jihar Ogun.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Lanre Bankole, ne ya bayar da umarnin kamen kan kowane nau’in abin hawa, musamman wadanda ke bin babban titin Legas zuwa Ibadan.
- Kisan dan kwallo ta tada kura a Jihar Ogun
- Gwamna ya zargi shugabannin APC da magudin zaben fid-da-gwani a Jihar Ogun
“A duk lokacin da aka samu cinkoso a kan manyan hanyoyinmu sai masu ababen hawa su bar hannunsu, su koma daya hannun, wannan rashin da’a ne da ke haddasa haddura,” in ji Kwamishinan.
Dangane da hakan Kwamishinan ya umarci kwamandojin shiyya, da turawan ’yan sanda da masu bayar da hannu a jihar da su damke masu kunnen kashi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ya fitar wacce kuma ya sa wa hannu.
Sanarwa ta kuma ce, za’a kame abin hawan da mai shi, sannan ya fuskanci hukunci.