✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara kama gidan rediyon BBC ta wayar salula a Najeriya

Masu amfani da wayar salula a Najeriya sun fara kama gidan rediyon BBC, Landan cikin harsunan Ingilishi da Hausa. Wata sanarwa da gidan rediyon BBC…

Masu amfani da wayar salula a Najeriya sun fara kama gidan rediyon BBC, Landan cikin harsunan Ingilishi da Hausa. Wata sanarwa da gidan rediyon BBC ya fitar a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce, masu sauraren rediyon na BBC a nan Najeriya za su iya kama shirye-shiryensa ta hanyar danna wata lambar waya, kamar haka: 01 4405 222. 

Gidan rediyon BBC ya hada gwiwa da wani kamfani ZenoRadio da ke kan gaba a hidimar taimakawa wajen ganin jama’a suna sauraren tashar rediyo a wayoyin salula, don samar da dama ta sauraren BBC, a duk lokacin da ake bukata da Ingilishi (zabi na 1) ko da Hausa (zabi na 2).
Sanarwar ta ce masu amfani da wayoyin salula za su iya sauraren shirye-shiryen rediyon da ake watsawa daga kowanne layin wayar salula a Najeriya, kai-tsaye cikin harshen Ingilishi dare da rana, sai kuma cikin harshen Hausa kai-tsaye da karfe 6:30 na safe da karfe 3:00 na rana da kuma karfe 8:00 na dare agogon Najeriya, kana a ci gaba da jin kowane shiri har zuwa lokacin da za a watsa shiri na gaba.
Sanarwar ta ce idan masu da wayoyin salula suka kira wannan lambar waya: 01 4405 222 da duk layin da suke amfani da shi a Najeriya, sai kuma su zabi harshen da suke da ra’ayi daga jerin zabin sauti (audio menu) da aka tanada. Sai dai kuma za su biya kudin kiran waya ga kamfanin da aka yi amfani da layinsa, domin sauraren shirye-shiryen na BBC, gwargwadon farashin kiran na waya na kamfanin da suke amfani da shi.
Editan sashin Afirka na BBC, Solomon Mugera, ya ce: “Lambar ta 01 4405 222 za ta samar da wata hanya mafi sauki ta sauraren shirye-shiryen rediyon BBC, wanda kafin yanzu yana iya samuwa ne kadai a Najeriya, ta hanyar kama tashar a akwatunan rediyo da intanet da tauraron dan Adam. Muna godiya da wannan ci gaba da aka samu, duk mai wayar salula a Najeriya yanzu zai iya sauraren rediyon BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya cikin harshen Ingilishi da Hausa a koyaushe.”
Sanarwar ta ce ta hanyar amfani da fasahar kamfanin ZenoRadio, gidan rediyon BBC ya bi wani ingantaccen mataki na kyautata hanyar da jama’a za su iya sauraren shirye-shiryensa, inda duk mai amfani da wayar salula daga cikin layukan salula miliyan 132 da ake amfani da su yau da kullum a Najeriya zai samu damar kama gidan rediyon da wayarsa.
“Godiya ga BBC da kamfaninmu, yanzu masu saurare za su iya kasancewa da shirye-shiryen BBC masu kayatar da su daga kowane layin wayar salula a kasar (Najeriya)”, inji Morris Berger, babban jami’in kamfanin ZenoRadio. Ya kara da cewa, “Kasancewar wannan shi ne kamun ludayinmu na farko a Nahiyar Afirka, muna alfaharin cewa za mu yi aiki tare da BBC a wannan shiri.”