✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara Gasar Wasannin Kwalejojin Ilimi ta Kasa

An fara gudanar da Wasanin Tsalle-Tsalle da Guje-Guje na Kwalejojin Ilimi na Kasa  Shiyyar Arewa maso Yamma da Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke…

An fara gudanar da Wasanin Tsalle-Tsalle da Guje-Guje na Kwalejojin Ilimi na Kasa  Shiyyar Arewa maso Yamma da Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano ke karbar bakunci.

Yayin da yake bude gasar Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano Alhaji Kabiru Ado Lakwaya ya bayyana  daukar nauyin gasar a matsayin wani sabon shafi na ciyar da harkokin wasanni gaba a tsakanin dalibai.

Kwamishinan ya yi alkawarin tallafa wa Kwalejin Sa’adatu Rimi da duk abin da suke bukata ta fuskar wasanni.

Shi ma a nasa jawabin Shugaban Shirya Gasar kuma Babban Sakatare a Hukumar Wasannin ta Kasa Dokta Muhamamad Tasi’u Nura ya yaba da tsare-tsaren da Kwalejin Sa’adatu Rimi ta yi wajen gudanar da gasar.

Ya yi kira ga daliban su dauki gasar a matsayin wata dama a gare su da za su nuna kansu don samun ci gaba a fagen wasanni.

A gasar wasan kwalon kafa da aka yi tsakanin Kwalejin Sa’adatu Rimi da FCE Zariya, Kwalejin Sa’adatu Rimi ta yi nasara da ci 4-0.

Sai FCE Kano ta yi nasarar a kan FCE Isah Kaita da ci 2-0.

A wasan kwallon raga (Bolley Ball) na mata FCE Bichi ta yi nasara a kan FCE Zariya da ci 3-0. Sannan FCE Bichi ta sake yin nasara a kan FCE Kano da ci 3-0.