Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Taraba ta tura jami’ai na musamman domin damko ’yan bindigar da suka bindige wasu jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma suka kuma dauke bindigoginsu.
Kakakin Rundunar, DSP David Misal ya shaida wa Aminiya cewa tuni rundunar ta fara aikin a Takum don kamo wadanda ke zargom tare da karfafa tsaro a duk hanyoyin yankin da ke fama da hare-haren a ’yan makonnin da suka gabata.
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
- Abin da ya sa aka umarci jihohi su dakatar da yin rigakafin COVID-19
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
’Yan bindigar da ake zargin Tibabe ne sun yi wa ’yan sandan biyu kwanton bauna tare da kashe su a wani shingen binciken ababen hawa a kan hanyar Takum zuwa Katsina Ala.
’Yan sanda hudu ke nan ake zargin ’yan bindiga daga Jihar Benuwai suka kashe tare da kwashe makamansu a cikin makonnin da suka gabata.
Wani binciken ya nuna kimanin mutum 17 aka kashe a hanyar Wukar zuwa Takum, Takum zuwa Kashinbila da kuma Takum zuwa Katsina Ala.
Wani mazaunin garin Takum, Malam Maiwada ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ana tsare da mutane 54 da ’yan bindigar suka sace kuma ana ci gaba da tattaunawa da wadanda suka sace su kan kudin fansa.
Ya ce an sace dukkan mutanen 54 din ne a kan hanyoyi uku wadanda yanzu haka zaba barazanar tsaro ga matafiya.