Gwamnatin Katsina ta fara bincike kan yadda aka sace miliyoyin Naira daga asusun gidan gwamnatin jihar.
Babban Daraktan Yada Labaran Gwamna, Al’amin Isah ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai ranar Alhamis.
- Abin da Buhari ya ce wa fasinjojin jirgin kasan da ’yan bindiga suka sako
- Kotu ta ci Shugaban ’Yan Sanda tarar N1m kan baje-kolin wanda ake zargi
Duk da bai bayyana ainihin adadin kudin ba, ya ce da gaske an saci kudin, kuma har sun shigo da ’yan sanda cikin lamarin domin bankado barayin.
Sai dai wata majiya mai tushe ta bayyana wa Aminiya cewa Naira miliyan 31 ne aka sace, kuma wadanda ake zargi na hannun ’yan sanda ana bincike.
Wannan dai shi ne karo na biyu da irin haka ta faru a jihar, domin ko a watan Janairun 2020, sai da wasu da ba a gano su wanene ba suka balle ofishin tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Mustapha Inuwa, suka sace Naira miliyan 16.
Ofishin nasa dai na cikin Sakatariyar Jihar ne, kuma kwana daya bayan haka aka kamo mai gadi da wasu jami’ai biyu da ke aiki a wurin.