Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ce ta soma bincike kan wani bidiyo da aka yada wanda ake zargin daliban makarantar Chrisland da ke Jihar sun yi wa abokiyar karatunsu mai shekara 10 fyade.
Kakakin rundunar a Jihar, SP Benjamin Hundey, ne ya bayyana haka a ranar Litinin, yana mai cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Abiodun Alabi, shi ne ya ba da umarnin gudanar da binciken.
- Sojoji sun kashe Kwamandan ISWAP a Tafkin Chadi, Ammar Bin-Umar
- Sanatan da ke wakiltar mazabar Buhari a Majalisar Dattawa ya koma PDP
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda a kwanan nan aka yada bidiyon wata dalibar makarantar ta Chrisland mai shekara 10 wanda aka yi zargin abokan karatunta sun yi mata fyade yayin wata tafiya da suka yi zuwa Dubai.
Sun tafi Dubai ne domin wakiltar makarantarsu a Gasar Wasannin Makarantu ta Duniya da aka gudanar a birnin Dubai din daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Maris da ya gabata.
Hundey ya ambato Kwamishinan ’yan sandan na cewa, binciken zai taimaka wajen gano hakikanin wadanda suke cikin bidiyon da aka yada da kuma wurin da abin ya faru.
Ya kara da cewa, binciken zai shafi har da zargin barazanar kisa da aka yi wa wani dalibin makarantar da kuma batun gwajin juna-biyu da aka yi wa wata daliba ba tare da sanin iyayenta ba.
A cewarsa, “An ja hankalin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas kan wani bidiyon fyade da aka yada a kafafen sada zumunta wanda aka yi zargin ya auku ne a tsakanin daliban makarantar Chrisland da ke Legas.”
Jami’in ya ci gaba da cewa rundunarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu aikata miyagun laifuffuka a Jihar, tare da cewa za su yi aiki da hukumomin da suka dace wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu.
Daga nan, ya ba da tabbacin za su yi aiki da gaskiya ta yadda za a yi ma kowa adalcin da ya dace.
Gwamnati Ta Rufe Makarantar Chrisland
A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Legas ta rufe Makarantar Chrisland har sai baba ta gani saboda abin da ya faru.
Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin wadda ta sami sa hannun hukumomin da suka dace, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ta ce, ana kan gudanar da bincike kan lamarin.
“Duba da zarge-zargen da aka yi, za mu tabbatar da an samu dukkan abin da ake bukata domin tabbatar wa al’umma kokarin gwamnatin Jihar wajen bai wa kowane yaro kariyar da ta dace, musamman kuma ba da cikakkiyar kariya ga dukkanin cibiyoyin kula da yara a fadin Jihar kamar dai yadda dokar bai wa kananan yara kariya ta jihar, No.EO/AA08 ta 2016, ta tanadar.”
Gwamnatin Jihar ta kuma yi gargadin duk wanda aka kama yana ci gaba da yada wannan bidiyon, za a garkame shi a kurkuku na tsawon shekaru 14.
Kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin makarantar da lamarin ya shafa ya ci tura, sai dai wani wakilin makarantar ya ce nan ba da dadewa ba za a fitar da cikakken bayani a hukumance.