✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An fara bincike kan mutuwar yaro bayan an yi masa allura a Legas

‘Yan sanda a Jihar Legas sun fara bincike kan mutuwar wani yaro mai shekara uku da ake zargin allurar da wata malamar asibiti ta yi…

‘Yan sanda a Jihar Legas sun fara bincike kan mutuwar wani yaro mai shekara uku da ake zargin allurar da wata malamar asibiti ta yi masa ce ta yi ajalinsa.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, Kakakin ‘Yan Sanda a Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a wani asibitin da ke yankin Ogombo a jihar.

Rahotanni sun ambato Hundeyin na cewa, duk da suna da labarin faruwar hakan, amma babu wani bayani a hukumance da aka yi musu kan batun.

Ya ce, “Lallai muna sane da batun. Mahaifin yaron ya zo ofishinmu amma ya ki ya rubuta bayanin komai.

“Su ma jami’an asibitin sun zo ba tare da sun rubuta kowane bayani ba. Hakan ya sa aka tura su Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar don fadada bincike kan batun,” inji shi.

Tun farko, an yada wani bidiyon da ya nuna mahaifin yaron da aka sakaya sunansa na korafi a kan yadda wata malamar asibiti ta yi wa dansa allurar da ta yi ajalinsa.