‘Yan sanda a Jihar Legas sun fara bincike kan mutuwar wani yaro mai shekara uku da ake zargin allurar da wata malamar asibiti ta yi masa ce ta yi ajalinsa.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, Kakakin ‘Yan Sanda a Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a wani asibitin da ke yankin Ogombo a jihar.
- Yadda rungumar kaddarar Ahmed Lawan ta kawo karshen zamansa a majalisa na shekara 24
- Mai kokarin sayar da ’yar cikinsa kan N20m ya shiga hannu a Binuwai
Rahotanni sun ambato Hundeyin na cewa, duk da suna da labarin faruwar hakan, amma babu wani bayani a hukumance da aka yi musu kan batun.
Ya ce, “Lallai muna sane da batun. Mahaifin yaron ya zo ofishinmu amma ya ki ya rubuta bayanin komai.
“Su ma jami’an asibitin sun zo ba tare da sun rubuta kowane bayani ba. Hakan ya sa aka tura su Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar don fadada bincike kan batun,” inji shi.
Tun farko, an yada wani bidiyon da ya nuna mahaifin yaron da aka sakaya sunansa na korafi a kan yadda wata malamar asibiti ta yi wa dansa allurar da ta yi ajalinsa.